Mataimakin kwamishinan ‘yan sanda ya rataye kansa a Ogbomoso

Mataimakin kwamishinan ‘yan sanda ya rataye kansa a Ogbomoso

Wani mataimakin kwamishinan ‘yan sanda na hukumar leken asiri da binciken manyan laifuka (FCIID), Gbolahan Olugbemi ya kashe kansa a garin Ogbomoso na jihar Oyo.

Rahotanni sun bayyana cewa an gano gawar DCP wanda ya taba zama mataimaki ga tsohon Gwamna Adebayo Alao-Akala a cikin gidansa tare da rataye a wuyansa.

Ko da yake, har yanzu ba a gudanar da cikakken bincike don gano musabbabin mutuwarsa ba, wata majiya ta shaida wa Vanguard cewa kamar ya kashe kansa ne.

Marigayin DCP Gbolahan Olugbemi, an ce ya zo gida ne domin bikin Easter, inda ya isa gidansa da ke kan titin Petros Academy, yankin Federal Low cost, ba tare da wani ya raka shi ba.

Marigayin wanda shekarunsa ya haura 50, shi ne mataimakiyar gwamna Adebayo Alao-Akala a zamansa na wata goma sha daya daga 2006-2007.

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa an killace gidansa sannan kuma masu goyon bayansa sun tsaya cak domin nuna alhininsu dangane da mummunan karshen jami’in.

Wani makwabcinsa ya ce, “Wani lokaci yakan zo gida da jami’an tsaron ‘yan sanda. A gaskiya na gan shi kwanan nan yana tuƙi da kansa zuwa cikin kyakkyawan katafaren gidansa.”

“Shi kadai muke gani a kusa. Ba a saba ganin danginsa tare da shi ba.”

Majiyar ta kuma bayyana cewa, mutumin ya dade yana fama da matsalar damuwa.

Saboda ingantaccen aikin ɗan sanda, an ba shi shawarar yabo don yadda ya tafiyar da zanga-zangar ENDSARS a 2020.

Kafin rasuwarsa, Olugbemi ya taba rike mukamin jami’in ‘yan sanda na yankin Ilupeju a Ajah, kuma ya kasance mataimaki na musamman ga tsoffin kwamishinonin ‘yan sanda biyu a jihar Legas.