‘Yan Kasuwar Kano Sun Koka A Yayin Da Farashin Kankara Ya Karye
Farashin kankara a cikin babban birnin Kano ya yi ragu daga Naira 700 zuwa 150 sakamakon hazo da sanyin yanayi da mazauna garin suka fara fuskanta tun ranar Lahadin da ta gabata.
A makon da ya gabata ne aka siyar da farar Kankara ta Santana” a tsakanin Naira 600 zuwa N700 yayin da aka siyar da ruwan Leda da aka fi sani da “pure water” a kan Naira 200 zuwa 300 sakamakon yawaitar bukatu da aka yi a lokacin Azumin Ramadan da ake amfani da shi.
Wani cak da LEADERSHIP ta yi a ranar Juma’a a wasu wurare a cikin birnin ya nuna cewa farashin kayayyakin ya ragu matuka kuma an sayar da leda“pure water size ice block” a tsakanin Naira 100 zuwa 150 yayin da kankarar “Santana size” yanzu ake sayarwa tsakanin N150 da N250 ya danganta da wurin.
Masu siyar da kayayyaki sukan saka buhunan su a gefen hanya tsakanin karfe 3.00 na yamma zuwa 6.00 na yamma.
Wata mai sayar da kankara a kan titin Katsina, Halima Aliyu, wadda ta fara sana’ar a shekara ta hudu, ta ce ta sayi buhu a kan kudi Naira 1,000 (N50 kan kowane buhun buhu) kuma tana sayar da ita kan Naira 2,000 a halin yanzu.
A cewar ta, a cikin makon da ya gabata ta sayar da shi kan kudi Naira 250 kowannensu wanda ya kai kusan N5000 kan kowacce buhu.
Ta ce a makon da ya gabata lokacin da yanayi ya yi zafi, ta sayar da farar kankara a kan kudi Naira 700, amma yanzu farashin ya fadi saboda yanayi da karancin bukata.
Umar Hamza, wanda ke gudanar da shagunan sanyi a Asada Small Scale Enterprise, ya koka da karancin tallace-tallace a yayin da ake samun sauyin yanayi.
Ya ce, “A kullum a makon da ya gabata ina tanadi buhunan pure water guda 300 a dakina na sanyi na sayar da komai kuma har yanzu ana bukatar. Mun sayar da Naira 2,000 kan kowace buhu, amma a wannan makon. ana siyar da shi a kan 700 kuma har yanzu ba mu sayar da shi ba sai washegari.