Yanzu-yanzu: ‘Yan bindiga sun kashe ‘yan sanda 5 da wasu 16 a Ebonyi, Benueq

Yanzu-yanzu: ‘Yan bindiga sun kashe ‘yan sanda 5 da wasu 16 a Ebonyi, Benueq

Wasu ‘yan bindiga sun kashe jami’an ‘yan sanda biyar a ranar Juma’a a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi.

Majiyoyi sun ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 5:00 na safe a gadar Ebya, daura da titin Hilltop/Nwoke.

Hakazalika, an bayar da rahoton cewa wasu da ake zargin makiyaya ne dauke da makamai sun kashe wani jami’in soja mai ritaya, da wasu 15 a ranar Alhamis da ta gabata a wani hari da suka kai a garin Wandor da ke yankin Mbaikyor a gundumar Mbalom na karamar hukumar Gwer ta Gabas a karamar hukumar Gwer ta jihar Benue.

An kuma bayar da rahoton cewa maharan sun kone gidaje sama da 50, bukkoki, gonaki da rumbunan abinci a wasu matsugunai 11 a harin.

Harin na baya-bayan nan dai ya zo ne kimanin shekaru shida bayan wani hari makamancin wannan da wasu makiyaya dauke da makamai suka kai a cocin St. Ignatius Catholic Church, Ukpor Parish, Mbalom Gwer East LGA, ya yi sanadin mutuwar wasu limaman cocin Katolika guda biyu da wasu mabiya coci 17.

Wani da ya tsira da ransa a harin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce ‘yan fashi da makami da yawansu ya kai 40 sun abka cikin al’ummar da misalin karfe 7 na dare inda suka bude wuta kan mutanen yankin da ba su sani ba.

Da take tabbatar da faruwar lamarin, shugabar riko ta karamar hukumar Gwer ta Gabas, Misis Comfort Agbo ta ce “a halin yanzu akwai zaman lafiya a yankin Wandor. Ya zuwa yanzu an gano gawarwaki 16. Biyu sun jikkata kuma suna karbar magani.

“Wadanda suka kai hari tare da kashe mutanena ana zargin makiyaya ne da makamai. Yanzu haka dai jami’an tsaro na kwashe gawarwakin zuwa dakin ajiyar gawa.”

Da aka tuntubi jami’ar hulda da jama’a na ‘yan sandan, Sufeto, SP, Catherine Anene wadda ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce kwamishinan ‘yan sandan na kan hanyarsa ta zuwa inda aka kai harin domin tantancewa a nan take.