Gayyatar ku Ba ta zo ta hanyar da ta dace ba – Abba Kabir Yusuf
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya Maida martani kan gayyatar da shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Umar Ganduje ya yi masa tare da wasu da su shigo jam’iyyar.
Yusuf, wanda ya yi magana ta bakin mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya ce Ganduje bai bi hanyar da ta dace ba.
Daily Trust ta ruwaito bayan taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a Kano a ranar Alhamis, Ganduje ya bukaci Yusuf ya yi watsi da jam’iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP) zuwa APC.
Ya ce, “Muna kira ga masu son shiga APC da su zo. Musamman muna gayyatar Gwamnan Kano da jam’iyyarsa ta NNPP zuwa APC.”
Amma da yake mayar da martani, Gwamnan ya ce, “Mun ji cewa yana rokon Gwamna ya koma APC, abin mamaki shi ne Ganduje a matsayinsa na tsohon Gwamna kuma tsohon Mataimakin Gwamna ya fi kowa sanin hanyar da ta dace wajen aika sako ga Gwamna mai ci. .
“Mai girma Gwamna (Abba Kabir Yusuf) ba shi da shirin barin jam’iyyarsa kuma ba zai bar jam’iyyar ba.
Canza jam’iyya kamar canza gida ne, ba za ku iya tashi ba, ku tattara kayanku ku ce na bar jam’iyyata. Akwai abubuwan da za ku yi kafin ku yanke shawarar canza gidanku,” in ji shi.