An gano gawa 5 cikin 100 da jirgin ruwa ya kife dasu a jihar Neja
An ba da rahoton bacewar fasinjoji da dama yayin da wani jirgin ruwa dauke da mutane kusan 100 ya kife a karamar hukumar Borgu ta jihar Neja.
Jami’in da ke kula da hatsarurruka na karamar hukumar Borgu a jihar, Malam Musa Said, ya bayyana cewa kawo yanzu an gano gawarwaki biyar yayin da ake ci gaba da aikin ceto da kuma ceto har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto.
Babban Daraktan Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, Abdullahi Baba Arah, ya tabbatar wa wakilinmu faruwar lamarin, inda ya ce har yanzu ba a kai ga tantance adadin wadanda suka mutu da kuma wadanda suka tsira da rayukansu ba.
Ya ce kwale-kwalen ya taso ne daga Dugga Mashaya da ke unguwar Dugga a karamar hukumar Borgu ya nufi kasuwar Wara da ke Jihar Kebbi tare da fasinjoji kusan dari da kayayyaki, kamar hatsi da rake.
Arah ya ce, “NASEMA ta samu rahoton hatsarin jirgin ruwa da ya afku a karamar hukumar Borgu. Lamarin ya faru ne da yammacin yau Litinin 15 ga watan Janairun 2024 da misalin karfe 2:05 na rana
Babu takamaiman bayani game da mace-mace da waɗanda suka tsira tukuna. A halin da ake ciki, ana ci gaba da aikin bincike da ceto daga masu ruwa da tsaki na yankin, da jami’an hukumar NSEMA, da jami’an kananan hukumomi. Za a gabatar da sabuntawa kamar yadda aka karɓa. “
Sai dai wasu majiyoyi da ba a tabbatar da su ba sun alakanta lamarin da igiyar ruwan kogin da kuma wuce gona da iri.
Jihar Neja dai ta fuskanci hatsarin kwale-kwale da dama a cikin ‘yan watannin da suka gabata lamarin da ya janyo asarar rayuka da dama.
Lamarin na baya-bayan nan shi ne a watan Nuwamban 2023 a karamar hukumar Shiroro inda aka yi asarar rayuka akalla 10.