Kotun Koli ta tabbatar da zaben Sanwo-Olu

Kotun Koli ta tabbatar da zaben Sanwo-Olu

Kotun koli ta tabbatar da zaben gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas. Jam’iyyar Labour (LP) da dan takararta, Gbadebo Rhodes-Vivour, sun kalubalanci…

Kotun koli ta tabbatar da zaben gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas.

Jam’iyyar Labour Party (LP) da dan takararta, Gbadebo Rhodes-Vivour, sun kalubalanci nasarar Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), amma sun sha kaye a kotun koli da daukaka kara.

Jam’iyyar LP ta bukaci kotun kolin da ta tabbatar da cewa zaben na ranar 18 ga watan Maris ya tafka kura-kurai, da rashin bin dokar zabe, inda ta kara da cewa mataimakin gwamna Obafemi Hamzat bai cancanci tsayawa takara ba.

Sai dai lauyan Sanwo-Olu, Nas Ogunsakin, ya bukaci kotun da ta yi watsi da kararrakin, ganin cewa wadanda suka shigar da karar ba su gabatar da shaidun da za su tabbatar da ikirarin nasu ba, kuma shaidun da aka kawo ba su da kwarewa.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne wani kwamitin alkalai bakwai karkashin jagorancin mai shari’a Mohammed Garba Lawal ya yi fatali da karar da Rhodes-Vivour ya shigar.