Mutane 200 ne suka mutu, suka jikkata a harin da Isra’ila ta kai a rana guda
Falasdinawa 73 ne suka mutu sannan 99 suka jikkata a hare-haren da Isra’ila ta kai a Gaza cikin sa’o’i 24 da suka gabata, in ji ma’aikatar lafiya.
WHO ta ce “ba a san inda majiyyata 600 da ma’aikatan lafiya suke a asibitin al-Aqsa na Gaza ba.”
Da yake magana daga Qatar, Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya ce zai tadawa Isra’ila “bukatar yin duk mai yiwuwa” don kara yawan kayan agaji.
Akalla mutane 22,835 aka kashe – ciki har da yara 9,600 – a hare-haren da Isra’ila ta kai a Gaza tun ranar 7 ga Oktoba. Kimanin mutane 1,139 aka kashe a harin da Hamas ta kai Isra’ila a ranar 7 ga Oktoba.