Yan Bindiga Sun Kona Mace Da ‘Ya’ya Biyu,da Surukarta A Sokoto
Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun kona wata uwa da sirikinta da kuma ‘ya’yanta biyu da ransu a wani harin da suka kai a garin Sokoto.
An ce ‘yan bindigar sun kai hari kauyen Kurya da ke karamar hukumar Rabah a jihar Sokoto da misalin karfe 8:30 na daren Lahadi.
Rahotanni sun ce sun kashe mutanen kauyen 12 tare da sace mata 3 yayin harin.
Wani mazaunin yankin, Yusuf Garba ya ce daya daga cikin wadanda aka sace ta rasa mijinta a harin.
Daga cikin wadanda harin ya rutsa da su har da wata mata da ta kone kurmus tare da surukarta da kuma ‘ya’yanta guda biyu a cikin dakinsu,” inji shi.
A cewarsa, daga baya maharan sun yi wani kazamin fada da sojoji.
“Muna zargin su ma sun yi asara mai yawa saboda mun ga tabon jini a inda suka ajiye babura. Amma ka san ba sa barin gawarwakinsu a baya,” inji shi.
Sai dai rundunar ‘yan sandan ta tabbatar da mutuwar mutane bakwai yayin harin.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Sakkwato, ASP Ahmed Rufa’i, ya kara da cewa suna ci gaba da tattara alkaluman wadanda suka mutu.
Idan dai za a iya tunawa, a tsakanin ranar Alhamis da Asabar din da ta gabata, sojoji sun kubutar da mutane 66 da aka yi garkuwa da su, bayan sun kai farmaki dajin Gundumi da ke gabacin jihar.