Likud ya ce ba zai sake goyon bayan Netanyahu ba.
Kafofin yada labaran Isra’ila sun ruwaito cewa ministan tattalin arzikin kasar na da burin kalubalantar shugabancin Netanyahu na jam’iyyar Likud bayan kawo karshen yakin.
Nir Barkat, wani jigo a jam’iyyar dama ta Likud, ya ce “ba zai sake goyon bayan Netanyahu ba” saboda jam’iyyar “na bukatar sauyi”, in ji kafar yada labarai ta Isra’ila Kan.
“Bayan yakin, dole ne mu koma ga jama’a kuma mu sake amincewa da su,” in ji Barkat.
Rahoton ya kara da cewa Barkat ya tabbatar da aniyarsa ta neman shugabancin jam’iyyar a ganawar sirri.
Netanyahu ya fuskanci guguwar suka kan gazawar leken asirin da ya kai ga harin na ranar 7 ga Oktoba. Tun kafin kai harin dai ana binciken Netanyahu kan zargin cin hanci da rashawa, inda aka ci gaba da shari’ar a ranar Litinin.