Yan Bindiga Sun Kashe Mafarauta 18 A Taraba

Yan Bindiga Sun Kashe Mafarauta 18 A Taraba

‘Yan bindiga sun kashe mafarauta 18 a wani harin da suka kai a karamar hukumar Bali da ke jihar Taraba.

Mun samu labarin cewa an kashe mafarauta 15 a arangamar da ‘yan bindiga suka yi a wani yanki da ke kusa da garin Maihula a ranar Talata.

An tattaro cewa ‘yan bindigar da yawansu ya haura 200 sun yi yunkurin kai hari a garin Bali hedikwatar karamar hukumar Bali da wasu kauyukan da ke kewaye amma mafarautan sun yi kicibis da su.

‘Yan fashin, an kara tattara sun fi nagartattun makamai fiye da mafarauta da suka kai ga kashe mafarauta 15.

Wata majiya a yankin Musa Umar ta shaida mana cewa mafarauta 14 ne suka mutu a wurin fadan yayin da wasu mafarauta suka samu raunuka, daya kuma ya mutu a hanyar zuwa asibitin Jalingo wanda adadin ya kai 15.

Shugaban kungiyar mafarauta na jihar Taraba, Adamu Dantala ya shaida mana cewa an kashe mambobinsa 15 a wata arangama da ‘yan bindiga.

Ya ce ‘yan bindigar sun kuma yi wa mambobinsa kwanton bauna a kusa da garin Dakka a karamar hukumar Bali inda suka kashe mafarauta uku.

“Muna bukatar goyon bayan gwamnati da al’umma domin su cika mu mafarauta makamai domin ba a ba mu wani kudi don tallafa wa iyalan wadanda aka kashe ko kuma jinyar wadanda suka jikkata,” in ji shi.

Masarautar Kur Bali, Alhaji Mahamud Abubakar, inda aka kashe mafarauta 15 ya shaida wa Aminiya cewa ‘yan bindigar sun mamaye masarautarsa ne tare da yunkurin mamaye garin Bali amma mafarauta suka tare su inda suka kashe mafarauta 15.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Usman Abdullah bai amsa kira ko amsa SMS da wakilinmu ya aike masa kan lamarin ba.