‘Yan Bindiga Sun Sace Daliban Jami’ar Jihar Katsina
Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun kai farmaki a dakunan kwanan dalibai na jami’ar tarayya da ke Dutsinma (FUDMA), jihar Katsina, inda suka yi awon gaba da dalibai mata guda biyar.
lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Laraba, a dakunan kwanan daliban da ke bayan makarantar Mariamoh Ajiri, kusa da Kasuwar Laraba a Dutsinma.
Daya daga cikin daliban jami’ar ya shaida wa wakilinmu ta wayar tarho cewa: “An yi garkuwa da biyar daga cikinsu (daliban) ’yan jihohin Kano da Nasarawa ne kuma biyu daga cikinsu daliban jami’ar ne.
Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, babu wani bayani dangane da halin da wadanda abin ya shafa ke ciki domin wadanda suka yi garkuwa da su ba su tuntubi iyalansu ba.
Dalibai sun tabbatar da cewa, bayan wani abu makamancin haka da ya faru a jami’ar tarayya da ke Gusau a jihar Zamfara, hukumar ta FUDMA ta umurci dukkan daliban su da su kasance a gida daga karfe 10 na dare.
Shugaban sashin hulda da jama’a na jami’ar Habibu Umar Aminu ya tabbatar da cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe biyu na safiyar ranar Laraba, inda ya kara da cewa ana ci gaba da kokarin kubutar da wadanda lamarin ya shafa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, ASP Sadiq Aliyu Abubakar, ya ce an kama mutum daya da ake zargi da bayar da bayanai ga ‘yan ta’addan.
Ya bayyana cewa an kuma kama wasu mutane da ake zargin suna da hannu wajen yin garkuwa da su.
Aliyu ya ci gaba da cewa, an yi hadin gwiwa wajen ganin an ceto daliban ba tare da samun matsala ba.