Kassim Shettima zai wakilci shugaba Tinubu a taron G77+ China.
Mataimakin shugaban kasa Kassim Shettima ne zai wakilci shugaban kasa Bola Tinubu a taron shugabannin kasashen G77+ China.

Shettima zai bi sahun sauran shugabannin kasashen duniya ciki har da Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres a wajen taron don tattaunawa kan batutuwan ci gaban da suka fi fuskantar mambobin kasashen kudancin duniya a birnin Havana na kasar Cuba.

P.S. G-77 gamayyar kasashen duniya 134 ne masu tasowa. Ita ce taro mafi girma na gwamnatocin kasashe masu tasowa a cikin tsarin Majalisar Dinkin Duniya, Yana ba da hanya ga kasashen Kudancin Duniya don bayyanawa da inganta muradun tattalin arzikinsu tare da samar da ingantacciyar damar yin shawarwari tare a Majalisar Dinkin Duniya.