Labaran Safıyar Yau

Ministan tsaro, Abubakar Badaru, ya roki ‘yan Najeriya da su ci gaba da taimaka wa gwamnati da addu’o’i na musammn a bangaren tsaron kasa.

Kakakin majalisar wakilai, Tajudden Abbas, ya ce, Najeriya tayi asarar naira tiriliyan 16.25 sakamakon satar danyen mai a tsakanin shekarar 2009 zuwa 2020.

Mutum 30 sun halaka a ruftawar kasa Kuje tare da garkuwa da mutum 19 a yankin Bwari da ke Abuja.

Zaɓen 2023: Atiku da Peter Obi za su ɗaukaka ƙara zuwa kotun ƙoli.

Shugaban hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Sheikh Daurawa, ya ce za a yi kidan ƙwarya da na shantu domin nishaɗantar da zawarawan da za yi bikinsu a Jihar.

Amurka ta dauke wasu daga cikin dakarunta daga Yamai babban birnin Nijar zuwa yankin Agadez, a cewar Ma’aikatar Tsaro ta Pentagon.

Kotun Faransa ta amince a haramta wa dalibai sanya abaya.

‘Yan bindiga sun kashe mutum 64 a Mali.

Hankula sun tashi a Chadi bayan sojan Faransa ya kashe sojan ƙasar.

Kotu ta kama ɓarawon yara da laifi a Kenya.

Miji da mata sun ɓace bayan ambaliya ta share gidan shaƙatawarsu a Girka.

A karon farko tun shekarar 1995, Barcelona za ta yi kakar wasa ba tare da dan wasan da zai goya lamba 10 ba.

Amurka tace tattaunawar cinikin makamai ta yi nisa tsakanin Rasha da Korea ta Arewa.

Kungiyar JNIM ta dauki alhakin kashe sojojin Burkina Faso fiye da 50.

Al-Ettifaq ta yi lattin taya dan wasan Manchester United, Jadon Sancho, bayan da aka rufe kasuwar saye da sayar da ‘ yan kwallo ranar Alhamis.

Tsohon kocin, Brighton da Chelsea Graham Potter, mai shekara 48, ya yi watsi da bukatar Lyon na zama kocin ta.