Kungiyar Kwararrun likitoci ta kasa zata yi tiyata da bada magani Kyauta a Kano

Bayan kammala taron karawa juna sani da kungiyar kwararrun likitocin kasar nan da ake kira Medical and Dental Consultant da ake gudanarwa a dukkanin bayan shekaru biyu kuma a zaɓi wata jiha guda 1 tilo aje a yiwa wasu mutane aiki kyauta kuma a basu magani kyauta.

Twins Empire ta ruwaito cewar, yanzu haka dai an gudanar da wannan taro da waɗan nan likitoci suka saba yi, kuma an zabi jihar Kano wadda za’a gudanar da aiki ga jama’a marasa lafiya waɗanda basu da karfin biyan kudin aiki ko kuma siyen maganin da za su cigaba da kula da lafiyar su.

Dr Bashir Yunusa Rano Kwararren likita ne a bangaren mafitsara, yace yanzu haka dai sun duba mutanen da basu da lafiya sama da 60 kuma sun zabi waɗanda za’a yiwa aiki kyauta daga cikin su.

Ya kara da cewar, kimanin mutane 1000 suke so zasu duba tare da yi musu aikin kyauta ba tare da sun biya kuɗi ba.

Dr Bashir yace aikin da za’ayi na kwana ɗaya ne kawai kuma da zarar an gama mutum zai iya komawa gida domin cigaba da shan maganin da aka bashi.

A nasu bangaren wasu daga cikin mutanen da suka rabauta da wannan aikin da kungiyar kwararrun likitocin kasar nan suka dauki nauyin aiwatarwa tare da hadin gwiwa da Alhaji Auwalu Abdullahi Rano, sun nuna jin dadi da kuma farin cikin su da samun nasarar yi musu aikin kyauta, inda suka ce lallai anyi musu wannna aiki ba tare da sun biya ko sisi ba, sun kara da cewar, matsalar kawai da suke fuskanta bai wuce jinin da za’a ƙara wa wasun su ba.

Shugaban ƙaramar hukumar Rano Hon Dahiru Muhammad ruwan kanya ya yaba da kokarin likitocin da suka dauki nauyin gudanar da wannan aiki tare da mika godiya ta musamman ga Alhaji Auwalu Abdullahi Rano.

Ya kara da cewar, matuƙar aka samu irin wannan aiki nan gaba ƙaramar hukumar zata samar da wasu abubuwan da ake bukata ba tare da an samu matsala ba.