Dan Sahu Ya Samu Karramawa
Ƴan Sandan Kano Sun Tabbatar Da Miƙa Wa Mamallakin Kuɗin Da Matuƙin Adaidaita Sahu Ya Tsinta
Rundunar ƴan sandan jahar Kano ,ta miƙa wa mamallakin kuɗin nan da wani matuƙin baburin Adaidaita sahu ya tsinta a Kwanar Dawaki a jahar kuɗin sa.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne , ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar tare da rabawa manema labarai a birnin Kano.
Sanarwar ta ce, mamallakin kuɗin ya yi cikekken bayani da kuma tambayoyin da jami’an ƴan sandan suka yi masa , ya tabbatar da cewa nasa ne inda aka miƙa masa kuɗin naira dubu ɗari uku da talatin.
Kwamishinan ƴan sandan jahar Kano CP Muhammad Usaini Gumel ya bawa matuƙin Adaidaita sahun kyauta ta girmamawa bisa gaskiyar da ya nuna.
matuƙin baburin Adaidaita sahun bayan ya tsinci kuɗin ya kaisu ofishin ƴan sanda na unguwar Fagge dan yin Cigiya.
Kwamishinan ƴan sandan ya godewa al’ummar jahar Kano ,ya godewa jama’ar jahar bisa haɗin kai da goyon bayan da suke basu a koda yaushe tare da kira da ayi koyi da bawan Allah.