Sojojin Nijar sun shiga Mali ne domin farautar ‘yan ta’adda — ma’aikatar tsaro

Ma’aikatar tsaron Nijar ta ce a ranar Juma’a sojojinta sun kashe ‘yan ta’adda 79 a wani samame da suka kai a makon da ya gabata a makwabciyar kasar Mali.
Dakarun rundunar yaki da jihadi ta Almahaou sun fara gudanar da bincike bayan da wata kungiyar ta’addanci dauke da makamai ta kai musu hari a yammacin garin Tiloa a ranar 10 ga Maris, in ji ma’aikatar.
Hakan na zuwa ne bayan da aka kashe akalla sojojin Nijar 17 a watan da ya gabata a Intagamey, wani gari a babban yankin Tillaberi da ke yammacin kasar, daya daga cikin yankuna da dama da ke karkashin dokar ta baci a halin yanzu sakamakon hare-haren ‘yan jihadi.
Ma’aikatar ta bayyana cewa, sojojin na sama da na kasa ne suka kai harin zuwa yankin Hamakat na kasar Mali, inda ake zargin wanda ya kai harin na ranar 10 ga watan Fabrairu.
Wata majiyar tsaro da ta tuntubi AFP ta ce tsawaita aikin a Mali “ba a taba ganin irinsa ba”.
Ma’aikatar ba ta bayar da rahoton asarar rayuka da sojoji suka yi ba a yayin farmakin.
An kai harin ne a Tillaberi, wanda ke kan iyaka da Burkina Faso da Mali – kasashe biyu da ke fama da hare-haren masu jihadi.
Tun a shekarar 2017 ne yankin ya sha fama da hare-hare daga kungiyoyi masu dauke da makamai masu alaka da Al-Qaeda da kungiyar IS.
A farkon watan Maris, shugaban sojojin Mali Kanar Assimi Goita ya tarbi babban hafsan hafsan sojin Nijar Janar Salifou Mody a Bamako.
Nijar ta ce sun tattauna batun hadin gwiwa kan tsaro a kan iyakar kasashen biyu sama da kilomita 800.
AFP