Kabarin wata yar Urar da aka binne tare da kayan ado da aka tono a Turkiyya
Tarihi da Tauhidi
An gano wani kabari na wata ‘yar kasar Urar mai daraja da aka binne tare da kayan adonta a katanga Çavuştepe da ke gundumar Gürpınar na lardin Van na gabashin Turkiyya.
An yi jana’izar wannan mata da cikakkun kayan adon kaya masu kyau.
A wata hira da kamfanin dillancin labarai na Anadolu, farfesa Rafet Çavuşoğlu, shugaban sashen ilmin kimiya na kayan tarihi na jami’ar Van’s Yüzüncü Yıl, ya bayyana cewa, sun gano muhimman bayanai a yankin necropolis a tsawon shekaru uku da ake gudanar da aikin.
Çavuşoğlu ya yi nuni da cewa wannan ba shi ne karo na farko a wannan shekarar ba da aka tabbatar da muhimmancin kayan ado a cikin al’adun binne mutanen Urar, Çavuşoğlu ya ce: “Wannan kabari na karshe da muka tono mai yiwuwa na wata mace ce mai shekaru 20-25.
Abin da ke da muhimmanci a nan shi ne, an binne matar da dukkan kayan adonta. Akwai kusan cikakkiyar kayan ado a kan kwarangwal ɗinta, wanda ke nuna cewa an yi la’akari da al’adun ado na matan Urar. (Anadolu Agency).