Tinubu Ba Zai Musuluntar da Najeriya ba – Masari

Gwamnan jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, ya bayyana ikirarin cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu, zai musuluntar da Nijeriya idan aka zabe shi shugaban kasa a 2023 a matsayin mara tushe.

Da yake magana a ranar Talata a wani taron gari da kungiyar Kiristocin Arewa ta Siyasa a lokacin da suka tarbi uwargidan Tinubu, Sanata Remi Tinubu, a Kaduna, Masari ya ce ko makaho ne zai zabi Tinubu idan ya hadu da wasu ‘yan takarar shugaban kasa.

Masari ya bayyana jihar Legas a matsayin karamar Najeriya, inda ya ce Kiristoci da Musulmi da ma arna duk suna zaune a Legas amma duk da haka Tinubu ya kai.

“Ba shi da tushe balle makama a bayyana tsoron cewa Tinubu zai musuluntar da Najeriya. Ba gaskiya bane. Shin Buhari ya musuluntar da Najeriya bayan shekara bakwai yana mulki? Shin Obasanjo ya komar da Najeriya Kiristanci bayan shekaru takwas yana mulki? Shin Jonathan ya mayar da Najeriya kasar Kirista bayan shekaru shida yana mulki?

A nasa jawabin, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya ce babbar matsalar kasar nan ita ce siyasa da dacin rai.

Ya bayyana cewa idan matasa maza da mata za su taru domin wani aiki na bai daya ba tare da dacin rai ba za a samu fata ga kasa.

“Tarihi zai maimaita kansa. A lokacin mulkin soja karkashin Janar Ibrahim Babangida ya koma mulkin farar hula, an yi zabe tsakanin MKO Abiola da Alhaji Bashir Tofa na SDP da NRC. Abokin takarar Abiola musulmi ne. Tikitin takarar musulmi da musulmi ne ya lashe zaben. Tofa wanda ya zabi abokin takarar Kirista ya sha kaye a zaben. Don haka Tinubu ne zai ci zabe,” inji shi.

Shi ma da yake jawabi, gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-rufai, ya ce gwamnonin APC na arewa sun yanke shawarar marawa dan takarar shugaban kasa a kudancin kasar baya “domin hadin kai, daidaito da adalci a kasar nan.

“Bayan mulkin shugaba Buhari, ya dace fadar shugaban kasa ta tafi Kudu. Kuma mun yi taro a Katsina Lodge a gaban Gwamna Aminu Bello Masari inda ya ce a cikin dukkan masu neman takarar Shugaban kasa mu je wa Ahmed Tinubu saboda irin nasarorin da ya samu a lokacin da yake Gwamnan Legas.”

Sanata Oluremi Tinubu, ta ce mijinta ba zai kyale ‘yan Najeriya ba idan har aka zabe shi a karagar mulki, inda ta bayyana shi a matsayin ma’aikacin aiki kuma mutum ne mai “cike da hankali”.

Shugaban kungiyar matasan Kiristocin Arewa, Mista Isaac Abra, ya ce Tinubu ne ya fi kowa cancantar tsayawa takarar shugaban kasa saboda abubuwan da ya gabatar.