2023: Matar Atiku Ta Yi Alkawarin Samun Rayuwa Mai Kyau Ga Mata
Uwargidan Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa, kuma ‘yar takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Gimbiya Rukaiya, ta sha alwashin baiwa mata karfin gwiwa idan jam’iyyar ta karbi mulki a 2023.
Gimbiya Rukaiya, a wani taro da aka gudanar a garin, a wani bangare na yakin neman zaben dan takarar jam’iyyar PDP, ta ce za a horas da mata da dama domin su samu kwarewa.
“Na zo nan ne don tunatar da ku, in gode muku tare da neman wata alfarma a gare ku, idan zabe ya zo, don Allah ku goyi bayan mijina, ku goyi bayan Aishiru Kudan, dan takarar gwamnan jihar Kaduna da sauran ’yan takara a jam’iyyar People’s Democratic Party.
“Zan kuma dawo don karfafawa mata kuma zan bi unguwa-unguwa tare da daukar akalla mutane goma daga kowace shiyya domin karfafa su”.
Ta bayyana godiya ga mutanen Kaduna bisa goyon bayan da suka bai wa mijinta a zaben da ya gabata.
“Ina so in sake gode muku saboda jihar Kaduna ta zabi mijina da yawa a zaben da ya gabata; har ma da kansa ya fadi,” in ji ta.