Kotu ta aike da shugaban EFCC zuwa gidan yari

Mai shari’a Chizoba Oji na wata babbar kotun tarayya da ke babban birnin tarayya Abuja, ya bayar da umarnin aike shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC zuwa gidan yari bisa laifin ƙin bin umarnin kotu.

Alkalin ya kuma umurci Sufeto-Janar na ‘yan sandan kasar da ya tabbatar da an aiwatar da hukuncin.

Oji ya ba da umarnin ne a ranar 28 ga Oktoba, in da a ka raba wa manema labarai a Abuja kwafin umarnin.

AVM Rufus Adeniyi Ojuawo ya gabatar da korafi a kan gwamnatin tarayya mai lamba FCT/HC/M/52/2021 a kara mai lamba FCT/HC/CR/184/2016.

AVM Ojuawo ta bakin lauyansa R.N. Ojabo, ya nemi umarnin daure Shugaban Hukumar EFCC a gidan yari.

Hakan ya bayu ne bisa rashin biyayyarsa ga kotu, ya kuma ci gaba da bijirewa umarnin kotun da ta bayar a ranar 21 ga Nuwamba, 2018.

Kotun ce ta umarci EFCC, Abuja da ta mayar wa wanda ya shigar da korafi motsa kirar Range Rover (Supercharge) SUV da kudin ta ya kai Naira miliyan N40M