Labaran Yammacin Alhamis 29/09/2022CE – 03/03/1444AH Ga Takaitattun labaran.
Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi ‘yan takarar a zaben 2023 su guji keta rigar mutunci da tunzura jama’a a yakin neman zabensu.
NECO Ta Saki Sakamakon Jarabawar Kammala Sakandare Ta 2022.
Sheikh Abduljabbar Naisru Kabara, wanda ake zargi da yin batanci ga Annabi Muhammad (SAW) a karatuttukansa, ya zargi lauyansa da karbar Naira miliyan biyu daga hannunsa, don bai wa alkali a sake shi.
‘Yan takarar shugaba kasa a zaben 2023 na Najeriya sun sa hannu kan yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya a birnin Abuja.
Shugaban Majalisar Dattijai Sanata Ahmed Lawan ya ce ya karbi hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ya ce ba shi ne halattaccen dan takarar majalisar dattijai na jam’iyyar APC a mazabar Yobe ta Arewa ba.
Sarkin Lokoja Muhammad Kabir Mai Karfi III ya rasu.
Matashi ya kashe kansa bayan ya soki mahaifinsa da wuka a Zariya.
Kotu a Makurdi, Jihar Binuwai, ta ba da umarnin tsare wani magidanci mai shekaru 45, bisa zargin sayar da ’yarsa mai shekaru hudu kan Naira miliyan 20.
An shiga farautar maharan da suka kashe sojojin Najeriya biyar a Anambra.
Hukumar Kiyaye Haɗurra (FRSC) reshen Jihar Kogi ta tabbatar da mutuwar mutum takwas sakamakon haɗarin mota da ya afku a Akpa da ke jihar.
Mutane kusan 20 suka mutu a Moroko bayan sun sha wata barasa mai guba a wani kantin gefen titi da ke birnin Ksar el-Kebir na arewacin kasar.
‘Yan sanda sun kama ɗan firamare kan zargin bai wa malama alewa mai guba a Kamaru.
‘Yan wasan firimiya ne suka fi samun raunuka fiye da takwarorinsu na Turai