Takaitattun Labaran Safiyar yau Alhamis 22/09/2022CE – 25/02/1444AH
‘Yan Majalisa sun soki tawagar mutum 100 da Buhari ya kai Amurka domin taron MDD.
Majalisar Wakilai ta bukaci Babban Sufeton ’Yan Sandan Najeriya ya binciki zargin da ake yi wa dan kasar Chinan nan, Geng Quanrong, na kashe budurwarsa, Ummulkulthum Buhari, wacce aka fi sani da Ummita, a jihar Kano.
ASUU ta ce za ta hada kan jiga-jigan lauyoyi don daukaka kara, akan umarnin da kotu ta basu na komawa bakin aiki.
Mutum biyar sun nitse a ruwa a kokarinsu na tsere wa harin ’yan bindiga a kauyen Chakumi a yankin Babban Birnin Tarayya Abuja.
Ana zargin wani matashi da kashe abokinsa ta hanyar daba masa wuka a wuya saboda rikicin canji N300 da ya shiga tsakaninsu a jihar Legas.
Karyewar Gada Ya Jawo Asarar Rai A Zariya.
Gwamnatin jihar Bauchi za ta fara hukunta iyayen da suka hana yaransu karatu.
Shugaban Kasar Rasha, ya ce ba da wasa yake ba kan barazanar da ya yi ta amfani da makaman kare-dangi kan kasashen Yamma don ya kare kasarsa.
Akalla mutum uku aka rawaito sun mutu sakamakon fashewa mai karfi da ta auku a wani gidan abinci da ke Kabul.
An yi jana’izar sama da mutum goma da mayakan Boko Haram suka kashe a Nijar.
An yi karar Donald Trump da ‘ya’yansa kan zambar biliyoyin dala.