An Banked Malamai 5,665 da basu cancanta a makarantun firamare da sakandire ba
Gwamnatin Jihar Niger ta bankado wasu malamai 5,665 da basu cancanta a makarantun firamare da sakandire ba
Shugaban kwamitin kwararru kan kidayar malaman, Labaran Garba ne ya bayyana haka lokacin da yake gabatar da rahoton kidaya na bana ga gwamna Abubakar Sani Bello a gidan gwamnati dake Minna.
Ya ce daga cikin malamai 24,061 a makarantun firamare 3,135, 4,703 ba su cancanta ba, yayin da malamai 962 daga cikin 6, 870 a makarantun sakandire 498 da ke jihar su ma ba su cancanta ba.
Garba ya lura cewa ma’aikatan gudanarwa na ilimi na kananan hukumomi 1,276 ne suke da shaidar koyarwa.
Kwamitin ya ba da shawarar cewa a rika gudanar da kidayar malaman makaranta duk bayan shekaru uku domin samar da ingantaccen tsarin ilimi a jihar.
Da yake karbar rahoton, gwamnan ya baiwa kwararrun malaman tabbacin kulawa da su amma ya ce a fitar da wadanda ba su cancanta ba daga cikin tsarin ko kuma a ba su zabin komawa makaranta domin samun cancantar.
Ya yarda cewa malaman na fama da rashin kyawun yanayin aiki, ya kuma yi alkawarin ba su tallafin da ya dace domin kwadaitar da su.
“Yawancin malaman da ba su cancanta ba suna da yawa – sama da 4,000. Ya kamata mu fitar da su amma kuma za mu iya ba su zabin a horar da su su dawo,” inji shi.
Da yake yabawa kwamitin bisa kyakkyawan aiki, gwamnan ya umurci sakataren gwamnatin jihar (SSG), Ahmed Ibrahim Matane, da ya gaggauta kafa kwamitin aiwatarwa bisa shawarwarin kwamitin kidayar jama’a.