An sake samun bullar Ebola a Congo

Jami’an lafiya a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo sun ce an samu wata mata da ta kamu da cutar Ebola a lardin arewacin Kivu da ke kasar.

Matar mai shekara 46, ta mutu ne a ranar 15 ga watan Augustan da ya wuce a wani asibiti da ke Benni. 

Jami’an sun ce matar ta fara rashin lafiya a hankali daga nan kuma sai ta fara nuna alamomi na cutar Ebola a tare da ita.

Ana dai samun sake bullar cutar akai- akai a kasar abin da mahukunta suka ce abin damuwa ne.

A yanzu haka an tattara wadanda matar ta yi mu’amala da su don yi musu gwaji a kan cutar.

Jami’an lafiyar sun ce a yanzu haka akwai rigakafin cutar Ebola dubu guda a kasar, a in da a yanzu za a aika 200 zuwa Beni don dakile yaduwarta a garin.