An gudanar da wanke dakin Ka’abah
Hukumomi a Saudiyya sun yi bikin wanke Ka’abah bayan kammala aikin Hajjin bana.
Yarima mai jiran gado Muhammad bin Salman tare da shugaban masallatan Harami Sheikh Abdul Rahman da kuma Limaman Masallatan Haramin ne suka jagorancin wankin Dakin Allah.
Shafin intanet na Haramain, ya ce an gudanar da shi ne a yau Talata.
Ana amfani ruwan zam-zam da turaruka masu kamshi, ciki har da miski da kuma tawul mai tsabta wajen wanke dakin Ka’abah.
Akan tanadi dukkan abubuwan da ake bukata kwana guda kafin a wanke dakin.
Haka kuma ana shafe sa’oi biyu wajen wanke dakin.
Wanke dakin Ka’abah ya faru ne tun daga lokacin Annabi Muhammad (SAW).