Babu wani Hari da aka kai : SP KIYAWA

A jiya ne ake ta raderadin cewa ‘yan ta’adda sun kai Hari akan hedikwatar Rundunar shiyya ta daya dake kano, saidai a safiyar yau ne Kakakin Rundunar ‘yan sandar jihar kano ya bayyana cewa

“Babu Hari A Hedikwatar Shiyya ta ‘Yan sanda Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta musanta jita-jitar da ake yadawa a Kano game da harin da aka kai hedkwatar ‘yan sandan Najeriya shiyyar daya a Kano.

Jami’in hulda da jama’a na shiyyar a Kano SP Abubakar Zayyanu Ambursa ya tabbatar wa manema labarai hakan a Kano Ya ce yana cikin ofishin da wuri kuma ko bayan Sallar Juma’a na Sa’a guda da suka yi a Masallacin Zone ba a kai wani hari ba.

Da ya samu labarin haka sai ya fita ya sa ido a kan jami’an ‘yan sandan da ke aikin kofar shiga bayan Sallar Juma’a kuma abin da suke yi shi ne duban ababen hawa da aka saba yi da sauran tsare-tsare na tsaro bayan Sallar Juma’a.

Ya kuma bukaci jama’a da kada su firgita, su kwantar da hankalinsu domin babu wani hari da aka kai yankin”.