Bayan Barazanar Sace Shugaba Buhari ‘Yanbindigan Sun kai Hari Kan Jamian Fadar Shugaban

Kasa da sa’o’i 24 da ‘yan ta’adda suka yi barazanar yin garkuwa da shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan Kaduna Nasir El’Rufai a wani faifan bidiyo, wasu ‘yan bindiga dauke da makamai suka yi wa sojojin na Guards Brigade kwanton bauna a Abuja.

Sojoji uku ne suka jikkata yayin harin wanda ya jefa mazauna birnin tarayya Abuja cikin firgici.

‘Yan bindigar sun nufi makarantar koyon harkokin shari’a ta Najeriya da ke Bwari a lokacin da suka ci karo da jami’an sojojin.

Akwai rahotannin sirri daga majiyar sojoji cewa, ‘yan ta’addan sun dura babban birnin tarayya Abuja da nufin kai hari a makarantar koyon harkokin shari’a da ke Bwari da wasu cibiyoyin gwamnati.

Majiyoyin soji da suka nemi a sakaya sunansu sun ce harin na nuni da cewa ‘yan ta’addan sun mamaye birnin amma hukumomi sun ce saka ido kan motsin maharan.

A cewar daya daga cikin majiyoyin, wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun yi wa dakarun 7 Guards Battalion da ke sintiri a kan hanyar Kubwa zuwa Bwari kwanton bauna.

Ya kara da cewa sojoji uku ne suka jikkata yayin harin kuma an kwashe su zuwa asibitin THE domin kula da lafiyarsu.

Majiyar ta ci gaba da cewa: “Harin kwanton bauna da ya faru a yankin na Bwari ya nuna cewa a zahiri ‘yan ta’addan suna cikin yankin kuma mai yiwuwa ne su aiwatar da shirinsu na kai farmaki a makarantar koyon harkar shari’a da ke Bwari kamar yadda aka ruwaito a baya.”

Da aka tuntubi mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar soji, Kyaftin Godfrey Abakpa, ya tabbatar da cewa wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun kai wa sojoji hari amma an samu nasarar dakile su.

Ya kara da cewa an kwashe sojojin da suka samu raunuka zuwa asibiti kuma suna samun kulawa a yanzu.