Kungiyar kwadago ta fara gudar da Zanga-zanga don goyon bayan ASUU
Kungiyar kwadago ta Najeriya ta fara gudanar da zanga-zangar kwana biyu domin nuna goyon bayanta ga kungiyar Malaman Jami’o’in kasar ta ASUU da suka shafe watanni suna yajin aiki
Tuni dai kungiyar kwadagon ta umarci rassanta na jihohin kasar da su shirya gudanar da zanga-zangar kwanaki biyu domin nuna goyon bayansu ga kungiyar ASUU.
A jihar Kano ma tuni hadakar kungiyoyin kwadagon suka fito domin fara gudanar zanga-zangar
Kwamarate Ummu Khulsum Adamu daga kungiyar NLC reshen jihar Kano ta shaida wa BBC cewa suna zanga-zangar ne domin yaransu su koma makaranta.
Ta kara da cewa ”Muna son yaranmu su koma makaranta, saboda muna tsaron kar su zame mana ‘yan ta’adda, mun yi ne domin neman gwamnati ta duba bukakunmu”
Kamar yadda GANI YA KORI JI ta wallafa cewa A makon da ya gabata ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin kawo karshen yajin aikin cikin makonni biyu amma har kawo zuwa yanzu ba a sami matsaya ba tsakanin Gwamnatin Taraiya da Kungiyar ASUU.
Tun a ranar Litinin 14 ga watan Fabrairu ne kungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya, ASUU, ta tsunduma yajin aikin gargadi ga gwamanatin Najeriya na tsawon wata guda.
Yajin aikin malamai a Najeriya ya fi yin tasiri a kan dalibai wadanda ke tsintar kansu cikin damuwa, dalilin da ya sa wasu ke ganin ya kamata kungiyar ta sauya salon tunkarar rikicinta da gwamnatin kasar ba sai lallai ta hanyar yajin aiki ba.
A wani binciken da muka gudanar mutanen gari na nuna dar-dar na abin da ka iya zuwa sakamakon zanga zangar a bisa dalili na tsaro da ya addabi kasarnan.
Mutanen da mukayi hira dasu suna fatan cewa Allah ya sa a yi zanga zangar lafia tare da jan hankalin gwamnati data duba bukatan Kungiyar ta ASUU domin kawo karshen wannan yajin aikin