An yi na Budrwa ‘Yar Shekara 20 Fyade, Ta Rasu A Edo

Wata budurwa ‘yar shekara 20 mai suna Precious Aigbokhode, an zarge ta da yi mata fyade tare da cacccaka mata wuka a gidanta da ke jihar Edo.

An tattaro cewa lamarin ya faru ne a ranar 17 ga watan Yuli a Agenebode, karamar hukumar Etsako ta Gabas a jihar.

An tattaro cewa an daba wa marigayiyar wuka akai-akai kuma aka watsar da ita har ta mutu bayan wasu da ba a san ko su waye ba suka yi mata fyade.

AMINYA ta  ruwaito cewa an gano cewa an kama wani Zakariyya da laifin fyade da kuma kisa.

An kuma gano gawar marigayiyar a kan titin Pandaponti a cikin garin Agenebode inda aka jefar da ita.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Chidi Nwabuzor, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce Zakariyya yana taimakawa ‘yan sanda wajen gudanar da bincike.

Nwabuzor ya bayyana cewa wani Paul ya kai rahoto ga ‘yan sanda cewa an tsinci gawar kanwarsa Aigbokhode a kan titin Pandaponti.

“’Yan sanda sun je wurin da aka jefar da gawar, suka ga alamun tashin hankali; wuka da yawa sun daba mata a jikinta,” ya kara da cewa.

Ya ce an kwashe gawar zuwa dakin ajiyar gawa domin a tantance gawarwakin yayin da aka fara bincike na farko.