An Sace Matar Soja Da Sauran Mazauna Jihar Kaduna A Wani Sabon Hari a Kaduna
Harin dai a cewar mazauna yankin, ya fara ne da misalin karfe 11 na daren ranar Talata, inda ya dauki tsawon sa’a daya.
Wani mazaunin Keke A, da ya nemi a sakaya sunansa ya ce an yi garkuwa da akalla mutane uku a yankin.
Majiyar ta ce ‘yan bindigar sun kai hari a wani katon gida da ke yankin.
“’Yan bindigan sun zo ne da misalin karfe 11 na dare. Ina ganin babban burinsu shi ne wani katon gida da ke Keke A. Gidan na wani jami’in soji ne, amma a lokacin da aka kai harin, jami’in ba ya gida, sai masu garkuwa da mutanen suka shiga gidan suka dauko matarsa.”
“Sun kuma yi garkuwa da wani makwabcin jami’in sojan, hasali ma makwabcin an zabo shi ne tare da ‘yarsa ‘yar shekara takwas, amma suka jefar da diyar yayin da mahaifiyarta ta ci gaba da ihu da babbar murya.
“Ina ganin a lokacin ne suka fara harbe-harbe kai-tsaye don tsoratar da mutanen da za su yi tunanin kawo musu dauki, kuma a lokacin da duk abin da ke faruwa, sai wani mutum da ke komawa gida a cikin motarsa ya ci karo da masu garkuwa da mutane. Shi ne mutum na uku da aka tafi da shi,” inji majiyar.
Majiyar ta kuma ce mutane da dama da ke waje, ciki har da masu shagunan unguwar, sun gudu don gudun kada a yi garkuwa da su.
“Tun safiyar yau, mun ga takalma da yawa a kasa, kuma mun tsorata cewa takalman mutanen da aka sace ne. Amma, daya daga cikin mutanen da suka tsere daga harin ya shaida mana cewa takalman na wadanda suka gudu ne,” inji majiyar.
Sai dai wani mazaunin Keke B ya tabbatar wa da wakilinmu cewa an yi garkuwa da wani mutum, matarsa da wasu masu aikin gidan su biyu.
Ya ce, “Ina dawowa gida ina wanka sai na fara jin karar harbe-harbe. Daga baya na samu labarin cewa an yi garkuwa da wani mutum da matarsa da kuma ‘yan matan gidansu biyu a Keke B.
“Na firgita sosai. Na fito daga bandaki ba zato ba tsammani na kashe dukkan fitulun gidana. Harbin harbin ya yi kusa; kamar ‘yan fashin suna cikin harabar gidana.”
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna (PPRO), DSP Muhammad Jalige, ya ce zai dawo wurin wakilinmu amma bai yi haka ba har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto.