An Kashe Sama Da Masu Hakar Zinariya 100 A Inji Gwamnatin Chadi

Rikicin da aka yi a makon jiya tsakanin masu hakar zinare a arewacin kasar Chadi ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 100, in ji gwamnatin kasar.

Rikicin ya faru ne a ranakun 23 da 24 ga watan Mayu a gundumar Kouri Bougoudi da ke kusa da kan iyaka da Libya. Wurin dai yana da tarin ma’adanai da ba a sanya doka ba inda mutane ke neman zinariya.

Ministan tsaron kasar Chadi ya fada a jiya litinin cewa, a wani bincike da gwamnatin kasar ta gudanar, an kashe mutane fiye da 100, yayin da wasu 40 suka jikkata a fadan.

Minista Daoud Yaya Brahim ya ce fadan ya barke ne da daddare a wuraren da ake hakar ma’adinai, amma bai bayyana musabbabin tashin hankalin ba.

Ministan sadarwa na kasar Chadi ya fada a makon da ya gabata cewa fadan ya kasance ne tsakanin Larabawa da suka tsallaka kan iyaka daga Libya da kuma al’ummar Tama wadanda suka fito daga gabashin Chadi.
Hukumomin kasar Chadi sun dakatar da ayyukan hakar ma’adinai na yau da kullun a Kouri Bougoudi tare da kwashe mutane daga yankin.

Kasar Chadi dai na da hannu wajen yaki da ta’addanci da kungiyoyin ‘yan tawaye wadanda ke barazanar hambarar da gwamnatin wucin gadin da dan marigayi shugaba Idriss Deby ke jagoranta. 

Sai dai babu wata alama da ke nuna cewa kungiyoyin ‘yan ta’adda ko masu aikata laifuka sun taka rawa a tashin hankalin ma’adinai.