‘Yan bindiga sun sace malaman coci a Katsina

Rahotanni daga jihar Katsina a arewacin Najeriya na cewa wasu ‘yan bindiga sun afka wa cocin Saint Patrick Catholic Church, da ke Gidan Maikambo, a karamar hukumar Kafur, tare da sace malaman coci guda biyu da wasu yara biyu.

A wata sanarwa da daraktan yada labarai na cocin Christopher Omotosho ya aike wa manema labarai da jaridar Premium Times ta samu, ya tabbatar da wannan labari .

Jaridar ta ambato shi ya na cewa: “Da tsakar dare ne ‘yan bindigar suka afka wa cocin, suka yi awon-gaba da babban limamin cocin Rabaran Stephen Ojapa, da mataimakinsa Oliver Okpara da wasu yara maza biyu da ke tare da su,sai dai kawo yanzu, ‘yan bindigar ba su kira iyalai ko cocin katolikar ba domin bukatar wani abu’’.

Mr Omotosho ya yi kira ga jama’a su sanya malaman cocin a addu’ar Allah ya kubutar da su.