Hassan Sheikh Mahmud ya lashe zaɓen SOMALIA

Tsohon Shugaban Somalia Hassan Sheikh Mahmud ya sake zamowa sabon Shugaban kasa, bayan da ya doke Shugaba mai ci wato Muhammad Abdullahi Farmajo a zaben da yan majalisa suka jefa kuri’a.

Magoya bayansa sun rika murna a babban birnin kasar wato Mogadishu.

Sai dai masu sharhi na ganin sabon shugaban kasar na da jan aiki a gabansa, lura da yadda tsananin rashin tsaro ya gurgunta kasar, musamman daga kungiyar Al-Shabab.

Baya ga rashin tsaro Somalia na fuskantar mummunan fari, da har Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa zai jefa al’umma cikin bala’in yunwa.

Sai dai da zaben nasa a yanzu Bankin bada lamuni na duniya zai cigaba da tallafa ma Somalia a karkashin wani shiri na agajin dala miliyan 400.

Sai dai babban aikin da ke gaban wanda zai yi nasara shi ne kwace iko da yawancin yankunan Somalia daga hannun kungiyar al-Shabab.

Kungiyar masu kaifin kishin Islama da ke da alaka da al-Qaeda na ci gaba da mamaye sassa da dama na kasar tare da kai hare-hare akai-akai a Mogadishu, da sauran wurare.

Akwai fosta na ‘yan takarar shugaban kasa a Mogadishu babban birnin kasar, duk da cewa babu kuri’ar jama’a

Gwamnatin tarayya dai na samun goyon bayan Tarayyar Afrika a yakin da take yi da al-Shabab, wadda ta tura mata dakaru 18,000, da kuma Majalisar Dinkin Duniya.

Ba a taba gudanar da zaben dimokuradiyya na mutum daya da kuri’a daya ba a Somaliya tun shekara ta 1969.

Wannan kuri’ar ta biyo bayan juyin mulki da aka yi , mulkin kama-karya da kuma rikici tsakanin jagororin mayaka masu tsattsauran ra’ayin Islama.

Rashin zaman lafiya na daya daga cikin dalilan da suka sa Somalia ta kasa gudanar da zabe kai tsaye.

Wannan shi ne karo na uku da ake samun damar gudanar da zaben shugaban kasa a kaikaice a kasar ta Somaliya kanta. An gudanar da wadanda suka gabata a makwabciya Kenya da Djibouti.

Su wanene suka yi takarar kujerar shugaban kasa?

An sanar da zagayen farko na zaɓen, kuma ƴan takara hudu ne suka tsallake. 

Sun hada Said Abdullahi Deni, shugaban yankin jihar Puntland wanda ya samu kuri’u 65. Da shugaba mai Mohamed Abdullahi Farmajo, da ya samu kuri’u 59.

Sai Hassan Sheikh Mohamud- tsohon shugaban ƙasa wanda ya samu kuri’u 52 da kuma Hassan Ali Kheyre, tsohon Firaminista mai kuri’u 47. 

Ana ganin zaɓen zai kai zagaye na uku idan har ba a samu wanda ya yi nasara ba.

Yadda aka gudanar da zaben?

A bara ne ya kamata a ce an gudanar da zaben lokacin da wa’adin shekara hudu na Mista Farmajo ya zo karshe. Amma bambance-bambancen siyasa da rashin zaman lafiya sun jinkirta zaben kuma shugaban ya ci gaba da rike madafun iko.

Su kansu ‘yan majalisar da ke zabar shugaban kasa, wakilai ne da manyan daulolin kasar suka zaba.

‘Yan Majalisar sun taru ne a wani katafaren filin jirgin sama da ke cikin sansanin Halane mai tsaro sosai . Wannan shi ne babban sansanin soji na Tarrayar Afrika a Somalia (Atmis), kuma akwai gidajen ofisoshin jakadanci da kungiyoyin agaji a ciki.

Za a kada kuria ne cikin sirri .

Majalisun dokokin biyu sun kada kuri’a a zagayen farko na zaben, inda manyan ‘yan takara hudu suka tsallake zuwa zagaye na biyu.

Duk wanda ya yi nasara a zagaye na biyu shi ne zai mulki kasar a cikin shekaru hudu masu zuwa.

Zabukan da suka gabata dai sun fuskanci zargin sayen kuri’u tare da rahotannin cewa ‘yan takara sun bayar da kudi domin samun goyon baya.

Abin da al-Shabab ta ce 

A zabukan baya, al-Shabab ta yi barazana tare da yin awon gaba da shugabannin hauloli tare da sokar kansu a kan abin da suke yi kallo da matsayin kuri’ar da ta sabawa adinin musulunci.

A wannan karon ba ta ce komai ba game da zaben ba, koda ya ke ana fargabar cewa mambobinta ko magoya bayanta cikin sirri sun nemi kujeru a majalisar dokoki domin yin zagon kasa ga tsarin mulkin na kasar.

Shugaban makwabciya Djibouti Omar Guelleh ne ya bayyana haka a bainar jama’a a shekarar 2020, lokacin da aka ambato shi yana cewa: “Ina tsoron kada mu zama majalisar dokokin da al-Shabab ke iko da su a fakaice domin samun goyon bayan wasu daga cikin ‘yan majalisar. “

Wasu masu shrahi na ganin Mista Guelleh yana kara gishiri a game da yuwuwar kungiyar al-Shabab ta samu gindin zama a majalisar dokokin kasar, amma ko shakka babu tana tasiri a siyasar Somaliya.

Kalubalen da ke gaban sabon shugaban kasa

Bayan barazanar da kasar ta ke ci gaba da fuskanta daga kungiyar al shabab da kuma bukatar korar mayakan, Somaliya na fama da fari da ya addabi kasashen yankin.

Hakan ya haifar da rikicin jin-kai inda ‘yan Somalia miliyan uku da rabi ke fuskantar barazanar yunwa mai tsanani, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Makiyaya da suka yi hasarar shanu na shigowa garuruwa da garuruwa suna neman hanyar tsira.

Kazalika kasar na fama da hauhawar farashin abinci da man fetur sakamakon yakin Ukraine.

Akwai matsin lamba don kammala aikin tsara kundin tsarin mulkin kasar da kuma tabbatar da an gudanar da zaben dimokuradiyya a cikin shekaru hudu masu zuwa.

Sai dai tun da dadewa masu kula da madafun iko a Somalia sun amince a gudanar da zabe na mutum daya da kuri’arsa a wannan shekara, kuma sun kasa cika alkawarin.