‘Yan bindiga sun kafa sansanoninsu akan tsaunukan dake zagaye da babban birnin Tarayyar Najeriya
Rundunar ‘Yan Sandan Babban Birnin Tarayyar Najeriya Ta Kaddamar Da Samame Akan Sansanonin ‘Yan Bindiga
‘Yan bindiga sun kafa sansanoninsu akan tsaunukan dake zagaye da babban birnin, daga inda kuma suke kaddamar da hare-hare akan mutanen da basu san hawa ba balle sauka a garuruwan dake wajen birnin.
A baya bayannan dai ‘yan bindiga da masu satar mutane sun yi kaka gida a wasu kan duwatsun dake sassan birnin musamman wuraren dake kan iyakar Abuja da wasu jihohi irinsu Kogi, Niger, Nasarawa da Kaduna al’amarin da ya tada hankalin Ministan Babban birnin kasar Muhammadu Musa Bello da ta kai ga har ya gudanar da taron gaggawa kan matsalar tsaro da wasu kusoshin tsaron birnin.
Jaridar Muryar Amurka ta rawaito cewa Kakakin Ministan Abubakar Sani ya shaida mata cewa yawan satar mutane da aika aikar ‘yan bindiga sune suka sa Ministan kiran taron kuma ya umarci jami’an tsaron da su yi duk mai yiwuwa don kawo karshen matsalar, inda a wancan lokacin kwamishinan ‘yan sandan birnin CP Sunday Babaji ya sha alwashin daukar sabbin dabaru don yiwa tufkar hanci.
Bisa ga dukkan alamu kuma wadannan sabbin matakai sun fara tasiri, domin kuwa mataimakin kwamishinan ‘yan sandan birnin Abujan DCP Ben Igwe ya ce biyo bayan bayanan sirri da suka samu dangane da maboyar ‘yan bindigar da masu satar mutane tuni sun fara kaddamar da kai farmaki a kan tsaunukan Yangoje da Chukuku dake yankin karamar hukumar Kwali inda suka lalata maboyar ‘yan ta’addan.
DCP Ben Igwe ya ce za a ci gaba da kai ire iren wadannan farmaki akan sansanoni na ‘yan bindigar har sai an tsarkake birnin daga miyagun.
A hirar shi da Muryar Amurka, masanin tsaro Dr. Kabiru Adamu babban Jami’i a cibiyar dake bincike kan tsaro wato BEACON ya yabawa ‘yan sandan, sai dai yayi fatan jami’an zasu fara aiki da kananan jirage marasa matuka na leken asiri da a baya sufeta Janar na ‘yan sandan kasar ya ce an samar don zakulo maboyar miyagun cikin sauki da kuma afka masu.