Ƙaruwar Masu Fitowa Takarar Shugaban Ƙasa Baya Bani Tsoro : Yahaya Bello
Gwamnan Jihar Kogi kuma dan takarar shugaban kasar Najeriya a APC, Yahaya Bello, ya ce bai tsorata ba da yadda masu fitowa takarar shugaban kasa suke kara yawa ba A cewarsa ba ya fargabar shirye-shiren yarjejeniyar da ake yi kuma yana da yakinin kasancewa mai nasara komai rintsin yadda aka shirya zaben dan takarar jam’iyyar APC Bello ya yi wadannan furucin ne a wani taron manema labarai a Abuja wanda Kungiyar Kamfen din shugabancin kasar Yahaya Bello ta shirya.
Dan takarar shugaban kasa kuma Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce ko fargaba ba ya yi akan yadda mutane da dama suke ta fitowa takarar shugaban kasa, The Punch ta ruwaito. Haka zalika, ya ce bai tsorata ba da shirye-shiryen yarjejenyar jam’iyya ba saboda yana sa ran kasancewa mai nasara a ko wanne irin mataki jam’iyyar ta dauka wurin zaben dan takara.
Wannan furucin nasa ya biyo bayan kwana daya da Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana kudirinsa na tsayawa takara da kuma jagoran APC, Bola Tinubu, wanda ya nemi goyon bayan gwamnonin APC akan shirinsa na tsayawa takara. Ya ce bai razana da irin gogewar masu tsayawa takarar ba Gwamnan wanda ya samu wakilcin kwamishinan labaransa, Kingsley Fanwo kamar yadda Vanguard ta nuna, ya kada baki ya ce: “Ban razana da irin gogewa da kuma irin hidimar da suka yi a baya ba. Sai dai ka kwatanta da abin da mutum yake yi yanzu, ina tunanin su ne ya kamata su razana a halin yanzu.
“Gwamnan ya samu gogewa kuma shekaru 6 zuwa 7 kenan da ya ke mulkar jiharsa. Muna da tabbacin zai yi wa Najeriya aiki na gani da fadi.” Ya ce za a tsayar da dan takaran da ya cancanta ne daga ko wanne bangare Ya ci gaba da cewa zai yanko maganar da gwamnan ya yi: “Gwamnan ya ce an haife shi a Arewa ta Tsakiya. An haife shi a dan kabilar Egbira. Ba ni na zabi zama Egbira ba. Ban zabi zama dan arewa ba. Don haka bangaranci bai dace ya dakatar da mutum daga takara ba.
“Muna yawan kawo hakan a siyasa. Amma ba ma kawo batun a wuraren aiki. Yanzu direban da zai kai ka Onitsha daga nan, me ne ne burinka akan shi? Ba kawai sanin idan direban kwarai bane? “A siyasa ana tambayar daga wanne yanki mutum yake? A shekarar 2023 lamarin zai sauya. Za a zabi wanda ya fi cancanta, jajircewa da kuma wanda zai gina kasa ne kawai. Babu wani batun dan kudu, arewa, Ibo ko Bahaushe.”