Kotu ta haramtawa KAROTA kamen goyo a babura masu kafa biyu : KANO

Kotu ta haramtawa hukumar kula da zirga-zirgar ababen Hawa Karota kamen masu goyo akan babura me kafa Biyu.

Haka kuma kotun tace haramun ne karotar su kara karbar kudin tara daga hannun kowane mai Babur Da Yayi Goyo a jihar kano.

Alkalin babbar kotun jiha me 14 dake miller road Hon.Justice Naser Saminu shine ya bayyana hakan a yayin da yake zartar da hukunci kan karar da Bello Basi,Lamin Ibrahim Adam,Ibrahim Abdullahi da suka shigar da karar hukumar ta karota bisa kama musu babura d akayi har kuma aka karbi kudin tara 2,000 a hannunsu.

Da yake yanke hukunci a wannan rana ta Litinin 28-2-2022 Justice Naser Saminu yace hukumar karotan zasu biya wadancan mutane 3 da suka karbi kudin tara a hannunsu har naira 500,000 ga kowannensu haka kuma karotan zasu biya su kudin kara naira 100,000 Justice Saminu ya haramtawa hukumar karota kamen goyon baburi me kafa biyu matukar dai ba haya akeyi dashi ba, ya kara da cewa daga yau ya haramta karotar su kara karbar kudin tara a hannun jama’a matukar ba kotu ce tayi tarar ba

Daga karshe Alkalin kotun yaja kunnen shugaban hukumar karota daya sani dokace ta kafashi kuma wajibinsa ne yayi biyayya ga dokar da ta kafashi

Al’ummar Jihar Kano sunsha Yin Korafi akan Yadda ake Cinsu Tara Da zarar Sun yi kuskure Batare Da Hukuncin Kotu Ba