Gwamnatin Legas ta rufe wata firamare bayan malami ya zane ɗaliba
Gwamnatin Jihar Legas ta rufe wata makaranta mai suna Unic Vilos Montessori sakamakon dukan wata yarinya mai shekara biyu da malamin makarantar ya yi har ya yi mata tabo.
Kwamashiniyar Ilimi ta Legas Folashade Adefisayo ta faɗa wa kafar talabijin ta Channels TV cewa wannan hanyar koyarwar ba ta dace ba saboda wadda aka doka ɗin jaririya ce.
A cewarta, gwamnati ta rufe makarantar ce bayan ta tabbatar da labarin sannan kuma an gano cewa makarantar ba ta da lasisi, tana mai cewa suna shirin dirar wa irin waɗan nan cibiyoyin.
Mahaifiyar yarinyar, Faustina Ohamadike, ta faɗa wa gidan talabijin ɗin cewa tun farko ba ta yi niyyar bayyana abin da ya faru ba amma da mai makarantar ya yi mata barazana sai ta ɗora labarin yarinyar a shafukan zumunta.
Rahotanni sun ce iyayen yarinyar da kuma malamin da ake zargin ya yi mata bulalar maƙota ne sannan kuma ginin makarantar na kallon ginin gidan nasu a yankin Maza Maza da ke birnin na Legas.