Mata 13,000 ne suka yi ɓarin ciki a Asibitin Murtala na Kano a 2021
Hukumomin lafiya a Kanon Najeriya sun ce ana samun ƙaruwar matan da ke yin ɓari a lokacin goyon ciki.
Alƙaluman baya-bayan nan sun nuna cewa cikin mata kusan 30,000 da suka je haihuwa sama da 13,000 ne suka yi ɓarin cikin.
Hukumomin sun ce rabin waɗanda lamarin ya shafa a Asibitin Ƙwararru na Murtala Muhammad ne, kuma mata masu ƙananan shekaru sun fi yawa a cikinsu.
Hajiya Iya Halliru mai kula da masu aikin jinya ce a A Kanon kuma ta yi wa Khalifa Shehu Dokaji ƙarin bayani kan hanyoyin da za a bi wajen kauce wa yin ɓarin.