‘Abubuwan da aka gano kan cancantar malaman firamare a Borno na da tayar da hankali’

Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ya bayyana abubuwan da aka gano a rahoton da aka mika masa kan jarrabar da aka yi wa malaman firamare na jihar da cewa abin tsoro ne matuka.

Farfesa Zulum ya bayyana hakan ne Alhamis din nan bayan da kwamitin da aka dora wa aikin yi wa malaman firamaren 17,229 na kananan hukumomin jihar 27 jarrabawar rubutu da karatu da kuma lissafi.

Binciken ya gano cewa daga cikin malaman 17,229 a fadin jihar 5,439 ne, wato kashi 31.6 cikin dari ne kawai suka cancanci koyarwa.

3,815, kashi 22.1 cikin dari ba su cancanci koyarwa ba kuma ma ba za a iya musu horo su iya aikin ba, kamar yadda rahoton ya nuna.

Sai dai kuma malamai 7,975 wato kashi 46.3 cikin dari ba su cancanci aikin ba sosai amma kuma za a iya horad da su su kware.

Kwamishinan Ilimi na jihar, Lawan Abba Wakilbe, shi ne ya gabatar da rahoton.

Akwai kuma kamar yadda rahoton ya nuna malamai 2, 389, kashi 13.9 cikin dari, wadanda suke koyarwa ba tare da wata takarda ta karatu ba sam-sam daga kowace makaranta ba.

Sai dai gwamnan na Jihar Borno ya bayar da tabbacin cewa duk da matsalolin da aka gano ba zai kori wadanda ba za su iya koyarwar ba, amma bisa shawarar kwamitin zai duba yuwuwar mayar da su wuraren da za su iya wasu ayyukan.