Faransa za ta fara janye dakarunta daga Mali
Faransa da ƙawayenta sun ce za su janye sojojinsu daga Mali, kasar da suka shafe shekara 10 suna yakar mayaka masu ikirarin jihadi.
Cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa da suka fitar (wadda ta hada da kawayenta na Turai da kasar Kanada), Faransa ta ce matakan da gwamnatin Mali take dauka sun tilasta musu ficewa daga kasar.
Shugaba Macky Sall na Senegal wanda ke tare da Shugaba Macron yayin da yake wannan sanarwar, ya ce “Idan aka yi la’akari da halin da ake ciki a Mali, mun fahimci dalilan da suka sa kasashen Turai da Faransa suka dauki matakan da suka dauka a kasar, ganin cewa al’amarin ya haifar da juyin mulki har sau biyu”.
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya musanta cewa Faransa ta gaza a ayyukan tabbatar da tsaro da ta yi a Mali.