Wani da ake zargi ɗan bindiga ne ya kubuta daga masu neman halaka shi
Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta kubutar da wani matashin yaro da mutanen gari ke kokarin babbakewa a dalilin zargin da ke masa cewa mai garkuwa da mutane ne.
Wannan abu ya auku ne a kauyen Oke dake jihar, Ogun.
PREMIUM TIMES ta ruwaito cewa ‘Yan sanda sun tsirar da mutumin ne adaidai matasa suna yi masa ribiti da sanduna bayan sun ɗaureshi tamau da igiya, suna kokarin rataya masa taya a wuya su babbake shi.
Mutanen sun ce tun da safiyar Talata da karfe takwas yake yawo kusa da wani makarantar firamare ba a gane me yake nufi ba.
A dalilin haka mutane suka taru suka yi masa duka saboda a zaton su ya zo ya saci yaran mutane.
Kafin a cinna masa wuta sai wani dake tare da waɗannan matasa ya ce a bincike shi ko yana da tabuwar hankali.
“Mutumin ya bani tausayi domin badun isowar jami’an tsaro bada tuni sun aika shi lahira. Allah yayi da saurarn rai a gaba.
Wani Habib ya ce da farko mutumin bai nuna alamun yana da matsalar tabuwar hankali ba domin yana amsa tambayoyin da mutane suka yi masa lamar mai natsuwa.
“Wata kila dukan da mutanen suka yi masa ne ya sa yake yi kamar yana da tabuwar hankali.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Abimbola Oyeyemi ya tabbatar cewa mutumin na fama da matsalar tabuwar hankali.
Oyeyemi ya yi kira ga mutane da su daina yin hukunci kai tsaye ba tare da sun sanar da jami’an tsaro ba.
Ya ce duk wanda aka kama yana haka zai fuskanci hukuma.