kowa ya zaro takobi ya ja daga : Kannywood
Hirar da ‘yar wasan Hausa Ladin Cima tayi da BBC Hausa cewa ana biyanta Naira Dubu Biyar Kacal idan tayi fim ya tada kura a masana’antar shirya fina-finan ta Kannywood.
Ladin Cima ta bayyana irin nasarori da kalubalen da ta shiga a rayuwa ciki har da korarta da akayi a rokunen gidajen gwamnati da take zaune a ciki sawon shekara da shekaru, da kuma cewa ana biyanta kudin da ba su haura naira dubu biyar ba idan tayi fim.
“Ina Kannywood amma abinda ake biyana daga dubu biyar ne zuwa dubu biyu, bani da kudin da zan iya tanadi har nayi wane abu babba wa kaina, yanzu hirar nan da muke da kai daga yin fim na fito kuma dubu biyu aka bani, cewar dattijuwa Ladin Cima.
Ta kara da cewa ta fara yin fim ne a Kaduna a shekarun 1970s bayan rasuwar mijinta a inda tayi ta tafiya duk sati daga Kano Zuwa Kaduna domin yin fim kuma fim dinta na farko shi ne Shaihu Umar
Ba’a biyan mu sai dai a bamu abinci amma saboda muna son muyi fim haka muke zuwa Kaduna duk sati domin yin Fim.
Maganar Ladin Cima ta tada hankalin mutane kuma tasa ana yiwa masana’antar ta Kannywood da Daraktoci da Furodusas da rashin tausayin tsofaffi irinsu Ladin Cima.
Daraktoci da Furodusoshi irinsu Ali Nuhu da Falalu Dorayi, sun barranta kansu daga rashin biyan yan fim yadda ya kamata kuma sun ce suna biyan Ladin Cima kudi har N40,000 idan tayi musu fim.
Amma mawakin tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi, Naziru Ahmad, yace abin da Ladin Cima ta fada gaskiya ne yace Furodusoshi da Daraktoci basa yi wa ƴan fim adalci shi ma ya shaida hakan yana faruwa a masana’antar ta Kannywood.
Mawakin yayi bayyana cewa ba biyan ƴan wasa ba kawai ne matsalar masana’antar, ” Ko kuma mace ce ace sai anyi abu da ita za a saka a fim”
Amma maganar mawaki Naziru ta tada kura a inda wasu yan fim suka fito suka nuna rashin jin dadinsu da kalaman na sarkin Waka, wasu ma har da Allah ya’isa.
Jaruma Suwaiba Abubakar, wacce akafi saninta da Makauniya tace shekarunta kusan goma sha biyar a Kannywood babu wani Darakta ko Furodusa da ya taba nemanta domin a bata dama ta shiga fim.
Suwaiba tace abinda mawaki Naziru ya fada ba gaskiya bane kuma bai yi musu adalci ba da yayi musu kudin goro, saboda haka ita a nata bangaren, “Allah ya’isa”.
Shima Furodusa Abubakar Maishadda, yace abinda Ladin Cima ta fada ba daidai bane saboda shima yana biyanta irin abinda su Ali Nuhu da Falulu suke biyanta.
Akan Naziru Sarkin waka, Maishadda yace bazasu saba ido su bar Naziru ya bata masana’antar tasu ta Kannywood suna ba saboda haka, daidai suke dashi duk abinda ya fada zasu bashi amsa.
Maishadda yayi kira ga Naziru da san cewa duk abinda ya zama ayau sanadiyar Kannywood ne, saboda Kannywood tayi masa Riga da wando.
Anasa martanin, Mustapha Nabraska, yace lokacin da aka kori Ladin Cima daga gidanta shi ne ya kama mata gidan haya kuma ya dauke nauyin abincinta duk bayan sati biyu yana saya mata abinci ya kai mata.
Nabraska yayi gogan zana ga Naziru cewa shi ma ba adali bane. Amma yayi kira ga yan Kannywood a fahimci a daina magana a social media.
Anasa jan hankali, Jarumi Nuhu Abbdullahi yace “Akwai bukatar duk lokacin da mutum zai yi magana ya yi adalci, Falalu Dorayi da Ali Nuhu sun ce ga yadda suke biyan Mama Tambaya kudin aiki, BBC Hausa ta tabbatar da hakan wurin ta.
“Naziru kafito ka yi kudin Goro baka kyauta ba. Sai ka yi musu adalci da ire-iren su da su ke biyan hakkin aiki yadda Yakamata.
“Wadanda kuma basa biyan hakkin mutane idan anyi mu su aiki harda “Dan’uwan ka” yana ciki sai kacigaba da yi mu su wa’azi, Allah ya shirye su! Inji Jarumi Nuhu Abdullahi.
Anata bangaren, Jaruma Nafisa Abbdullahi, tace A ko wane sana’a akwai matsaloli daban daban da mutane ke fuskanta, akwai Masu cuta, akwai Kuma Wanda ake cutarwa.
Tace zargin da Naziru Ahmad yayi, suna girma matuka da “ba’a daukan su da sanyi ko ah ina ne, ah ciki har da ‘Sexual Assault’ Wanda shine dalilin da ya sa na saka Kaina ah cikin abinda bai shafe ni ba….. Amma Kuma idan akayi la’akari da abinda ya fada, ya shafe ni tunda mace ce ni.
“Idan abinda yake fada Gaskiya ne Kuma yana da hujjoji da Kuma shaidu, ina cikin mutanen da suke so su san su waye Masu yin hakan! Tunda ya fadawa duniya cewa ga abinda ake yi, toh karshen adalci wa Wanda aka zalunta shi ne mu san su waye Kuma mu dauki Mataki akan su.
Domin a cikin Laws (dokoki) din mu na kasar nan da Kuma film industry din, babu inda sai anyi lalata da mace kafin asata a fim. Wadanda aka samu da laifin haka ya kamata a kamasu ayi musu hukunci, cewar Jaruma Nafisa Abbdullahi.
Daga Karshe Kuma, tace duk macen da ta san an taba ce mata ta bada kanta ayi lalata da ita saboda fim ta fito tayi magana ta kwatarwa kanta yanci saboda samun gyara ba.
Saboda dalilin da Jaruma Nafisa Abbdullahi ta bayar na dokar kasa dana Kannywood, PREMIUM TIMES HAUSA tayi kokarin jin ta bakin hukumomin Kano ciki har da Yan Sanda ko zasu yi bincike Kan wannan sabon takaddama ta Kannywood, amma hakan bai samu ba a yau.