Rasha za ta fuskanci martani mai zafi idan ta mamaye Ukraine : Biden

Kokarin kawo karshen zaman tankiya a game da rikicin Ukraine ta hanyar tattaunawa ta wayar tarho a jiya Asabar ya ci tura, inda ma shugaba Joe Biden na Amurka ya gargadi Rasha cewa za ta fuskanci martani mai gauni idan dakarunta suka aiwatar da alwashinsu na mamaya.

Shugaba Vladimir Putin ya caccaki ikirarin da kasashen yamma ke yi na cewa Rasha na shirin mamayar Ukraine, yana mai cewa tsokana ce da ka iya haddasa rikici a tsohuwar kasar ta Tarayyar Soviet, a cewar wata sanarwar da fadar Kremlin ta fitar bayan tattaunawarsa da shugaban Faransa Emmanuel Macron.

Zaman tankiya da aka shafe makonni ana yi sakamakon jibge dakaru samada dubu 100 a iyakar Ukrasine da Rasha ta yi ya ta’azzara, bayan da Amurka ta yi kashedin cewa Moscow za ta kaddamar da hare hare a kan Ukraine nan ba da jimawa ba.