Wata Kungiya Ta Baiwa Makarantu Horo Kan Dabarun Kare Kai
Ganin yadda hare-haren ‘yan-bindiga ya yawaita a makarantu a shekarar bara, ya sa wata kungiya mai zaman kan ta shirya taron bita ga Malamai da dalibai don kare kawunan su daka hare-haren.
Taron na yini guda ya tattara malamai da dalibai daga makarantu tara a jahar Kaduna inda masana su ka gabatar da mukala kan hanyoyin da za a bi waje tsira daga dukkan matsaloli masamman ma satar dalibai ko cin zarafin su.
Malam Isah Suleiman na kungiyar ‘Hope for the Community and Children Initiative’ na cikin wadanda su ka gabatar da mukala a wajen taron da Cibiyar Bincike kan Cigaba ta shirya a Kaduna.
“ Makarantu tara ne a nan, suna da wakilansu, fadakarwar zai basu daman sanin yadda za su kare kansu game da tsaro, kamar yadda ake daukar yara haka, akwai matakan da ya kamata a dauka saboda a samu saukin matsalar ko a magance shi gaba daya.”
Hajiya A’ishatu Mohammed dake kula da karatun dalibai mata a jahar Kaduna, ita ce ta wakilci ma’aikatar ilimi a wurin wannan taro.
“Gaskiya wannan shiri yayi daidai da wannan lokaci da muke ciki, maganar harkar tsaro ba abune da za mu sakawa gwamnati kadai ido ba, saboda haka tsakanin mu da iyaye da malamai da su jami’an ilimi inda suke Magana da kananan hukomomi 23 da suke Jaha domin tabbatar da cewa duk wani abu dake faruwa a makarantu da kuma dalibai cikin kankanin lokaci ya zama cewa hukuma tana sane da wannan abun.”
To ko wanne darasi Malamai da daliban da su ka halarchi wannan taro mai taken ‘Safe Schools Project’ su ka koya?
“Matsalolin da ake fama da su ta harkar tsaro, wanda yake shafar makarantu wannan taro yana inganta dabaru da kowa zai iya dauka domin tabbatar da yara dalibai, malamai da duk duk wanda ya shafi harakar karatuan samu an bada ilimi mai inganci ba tare da wasu matsalolin tsaro da ake fama da su ba.” In ji Malam Musa Shehu.
Jahar Kaduna dai ita ce kan gaba cikin jahohin da ‘yan-bindiga su ka fi kai hari a makarantu kamar yadda rahoton Asusun Tallafawa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) na shekarar bara ya bayyana.