Majalisar Tarayya ta fara shirin halasta wa matuƙa mota ‘yan sama da shekaru 21 yin amfani da ‘Bluetooth’

An gabatar da sabon ƙudirin halasta wa matuƙa mota yin amfani da ‘Bluetooth’ da sauran na’urorin sarrafa kira, amsa kira da sauraren kaɗe-kaɗe idan su na tuƙi.

Sai dai kuma ƙudirin idan ya samu karɓuwa, zai kasance sai matuƙin motar da ya haura shekaru 21 ne zai samu wannan damar a dokan ke kenan.

Ɗan Majalisa Ibrahim Hamza na APC daga Kaduna ne ya gabatar da ƙudirin, wanda ya amince da sai direbobin da su ka haura shekaru 21 a duniya ne dokar za ta amfana.

Shi dai wannan ƙudirin zai yi ƙoƙarin maye gurbin Sashe na 10 (4) na Dokar Hukumar Kare Haɗurra ta Ƙasa (FRSC). 

Shigo da dokar zai sa direba ya riƙa waya a lokacin da ya ke tuƙi, amma ta hanyar yin amfani da na’urorin da ba sai ya ɗaga waya ba.

Shi dai Sashe na 10 na Dokar Hukumar FRSC, ya bada umarnin su kama duk wanda su ka gani ya na amfani da waya a lokacin da ya ke tuƙi.

Shi kuma Sashe na 10 (4) ya tanadi kamawa da kuma bada umarni ga Jami’an Hukumar FRSC su gurfanar da wanda duk su ka kama ya na tuƙi kuma ya na waya a lokaci guda.

Wannan ƙudiri na so ya sauya alamar “ff” da ke jikin dokar, ya musanya shi da “gg”.

A cikin sabon ƙudirin, daga waɗanda ba a amince su yi amfani da wayar ba a lokacin su na tuƙi, sun haɗa da direbobin motocin ɗalibai, direbobin manyan motoci irin Roka, Shorido da Gindimari motar ɗaukar kaya. Akwai kuma direbobin manyan kaya irin su Turela da Tankin ɗaukar mai, ruwa ko wasu kayan nauyi.

Har ila yau, Hamza ya sake gabatar da wani ƙudirin da zai hana yin amfani da yatsan hannu wajen kullewa ko buɗe wasu ɓoyayyun bayanai. 

Hakan zai ba Gwamnanti ikon shiga cikin bayanan jama’a, domin binciken masu aikata wasu muggan laifuka ta yanar gizo.

Wannan ƙudiri dai na buƙatar tsallake wasu siraɗi biyu tukunna, kafin ya zama doka idan Shugaban Ƙasa ya sa masa hannu.