Gwamnonin arewa maso gabas sun ba wa Zamfarawa tallafin miliyan 20
Gwamna Babagana Umara Zulum na Jihar Borno a arewacin Najeriya ya kai ziyarar jaje Jihar Zamfara game da hare-haren ‘yan fashin daji na baya-bayan nan a madadin ƙungiyar gwamnonin arewa maso gabas.
Zulum wanda shi ne shugaban ƙuyngiyar gwamnonin, ya kai ziyarar ce a jiya Litinin a fadar gwamnatin jihar da ke Gusau.
Yayin ziyarar, gwamnan ya bai wa waɗanda tashin hankalin ya shafa tallafin naira miliyan 20. Cikin waɗanda suka yi masa rakiya har da Sanata Ali Ndume, Shugaban Kwamatin Sojan Ƙasa a Majalisar Dattawa, da Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Borno Abdullahi Musa Askira.
Da yake yi wa sarakunan gargajiyar yankin da kuma jami’an gwamnatin Zamfara jawabi, Gwamna Zulum ya nemi al’ummar jihar da kar su karaya, yana mai ambato irin ɓarnar da yaƙin Boko Haram ya haddasa a jiharsa ta Borno.