Ecowas ta saka wa Burkina Faso takunkumi
Rahotanni daga majiyoyi ta ɓangaren diflomasiyya sun tabbatar da cewa ƙungiyar ECOWAS ta dakatar da Burkina Faso daga ƙungiyar bayan juyin mulkin da aka yi a makon nan.
Ƙungiyar ta gudanar da tattaunawa ta bidiyo domin mayar da martani kan hamɓarar da Shugaba Roch Kabore.
A ranar Alhamis ne shugaban ƙasar na mulkin soji Sandaogo Damiba ya bayyana cewa Burkina Faso na buƙatar ƙawayenta na waje fiye da da.
Tuni ƙungiyar ECOWAS ta yi Allah-wadai da wannan juyin mulkin, wanda shi ne na uku a yankin da aka yi tun daga bara.
Tuni ƙungiyar ta ECOWAS ta saka takunkumi kan Mali da Guinea a yunƙurinta na ganin an mayar da mulki ga dimokraɗiyya.