Mali ta hana jirgin Jamus ketta sararrin samaniyarta
Gwamnatin mulkin soji ta Mali ta haramta wa wani jirgin soji na Jamus ketta sararrin samaniyarta a kan hanyarsa ta zuwa Nijar. Jamus dai na adawa da dorewar mulki soji a Mali.
Jirgin na rundunar sojojin Jamus wanda ke dauke da sojoji guda 80 da ya taso daga birnin Berlin, ya canza hanya ya sauka a tsibirin Kanari na Espain daga can ya isa Nijar. Jamus na da yawan sojoji sama da dubu daya da ke da sansani a Nijar da ke aikin tabbatar da tsaro a Mali, wadanda ke aiki tare a rundunar Takuba ta kasashen Turai da kuma Barkahn.Hukumomin Mali sun rufe kan iyakokinsu bayan da kungiyar Ecowas ta saka wa kasar takunkumi tare da rufe kan iyakokinsu saboda kin bayyana jadawalin sabon zabe da hukumomin Malin suka yi.