Alkaliyar Wasa ‘Yar Kasar Rwanda Ta Kafa Tarihin A Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka
‘Yar kasar Rwanda Salima Rhadia Mukansanga ta zama mace ta farko da ta yi alkalancin wasan Guinea-Zimbabwe a gasar cin kofin nahiyar Afirka.
Salima Rhadia Mukansanga ta shiga tarihi inda ta zama mace ta farko da ta taɓa alkalancin wasa a wasan gasar cin kofin nahiyar Afirka.
Mukansanga mai shekaru 35 ta jagoranci wasa na uku na rukunin B tsakanin Zimbabwe da Guinea a wannan Talata 18 ga watar Janairu 2022, a filin wasa na Ahmadou Ahidjo da ke Yaoundé.
Tana daga cikin mata hudu da aka zaba a matsayin alkalan wasa. Wannan dai shi ne karon farko da kungiyar ƙwallon ƙafa na Afirka ta yi irin wannan zaɓi a gasar cin kofin nahiyar Afirka tun da aka fara gasar.
Mataimakan Salima Radhia su ma dukan su mata ne. Carine Atemzabong na Kamaru da Fatiha Jermoumi daga Morocco da kuma alkaliyar wasa ta fasahar VAR Bouchra Karboubi ita ma ‘yar Morocco.
A ranar 10 ga watan Janairun 2022, mukansanga ta fara kafa tarihi inda ta zama mace ta farko da ta yi alkalancin wasa a gasar cin kofin nahiyar Afirka a matsayin alkalin wasa na hudu a wasan da aka yi tsakanin Guinea da Malawi a Bafoussam.
Daraktan alkalan wasa na CAF, Eddy Maillet ya yi la’akari da wannan lokaci mai cike da tarihi a matsayin sakamakon jajircewa da saka hannun jarin CAF na ingantawa da bunƙasa alkalan wasa a Afirka. Wani bangare na wannan tafiya shine “Star Project” da FIFA da CAF suka ƙaddamar don bunƙasa alkalan wasa.
Eddy Maillet ya ce “Muna matukar alfahari da Salima domin ta yi aiki sosai domin ta kasance inda take a yau. Mun san cewa ta fuskanci wasu matsaloli masu tsanani kafin ta kai ga wannan mataki, kuma ta cancanci yabo. Ya ƙara da cewa, :wannan lokacin ba na Salima kadai ba ne, a’a ga duk wata yarinya a Afirka da ke da sha’awar ƙwallon ƙafa kuma tana ganin kanta a matsayin alkalin wasa a nan gaba.”
Kada a manta Zimbabwe ce tayi nasa kan Guinea da ci 2 da ɗaya a wannan wasa.