Mali ta tsallake takunkumin MDD
Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya gaza saka sabon takunkumi a kan Mali sakamakon hawa kujerar na-ki da kasashen Rasha da China suka yi.
Kasashen Rasha da China sun hau kujerar naki tare toshe yunkurin Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan dankara sabon takunkumi a kan kasar Mali da ke yankin yammacin Afirka da sojoji suka yi banga-banga kan madafun iko, tare da dage zaben da aka shirya a watan gobe na Febrairu zuwa 2026.
Martin Kimani jakadan Kenya a majalisar ya ce an tattauna a kebence kan kudirin da Faransa ta gabatar domin amincewa da tsarin takunkumin kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS, kuma rashin amincewa da matakin na kungiyar ECOWAS ya bakanta ran kasashen Afirka uku da ke cikin Kwamitin Sulhu na Kenya da Ghana gami da Gabon.
Tuni manyan kasashen Yammacin Duniya irin Faransa da Amirka suka fara gangamin neman samun goyon baya daga kasashen duniya kan takunkumin da kungiyar ECOWAS ta saka kan kasar ta Mali, domin matsin lamba ga sojojin da ke rike da madafun ikon kasar kan hanzarta shirin mayar da kasar bisa tafarkin dimukaradiyya. Shugaban gwamnatin mulkin sojan kasar Kanar Assimi Goita ya ce suna shirye da ci gaba da tattaunawa da kungiyar ECOWAS amma ya ce takunkumin kungiyar ya saba ka’ida.